15 Faburairu 2022 - 16:23
EU Ta Bukaci A Kawo Karshen Tashe-Tashen Hankula A Unguwar Sheikh Jarrah A Gabashin Qudus

Kungiyar tarayyar Turai EU ta bukaci a kawo karshen tashe-tashen hankula a unguwar Sheikh Jarrah da ke gabacin birnin Qudus wanda ya zuwa yanzu sun yi sanadiyyar raunata Falasdinawa da dama, sannan jami’an tsaron yahudawa sun kama Falasdinawa da dama suka tsare.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -bayyana cewa an fara tashe-tashen hankula na baya-bayan nan ne, a lokacinda wani dan majalisar dokokin gwamnatin Yahudawa mai suna Itamar Ben Gvir ya bude majalisa a unguwar Shiekh Jarrah da nufin tattabatar da cewa an kori dukkan Falasdinawan da suke da gidajensu a unguwan don yahudawa su shiga gidajensu.

Tawagar kungiyar tarayyar Turai zuwa ga gwamnatin Falasdinawa ta bukaci a kawo karshen tashe-tashen hankulan ne a shafinta na Twitter. Tawagar ta zargi yahudawa masu tsatsauran ra’ayi da tada rikici na baya-bayan nan a unguwar.

A bangaren Falasdinawa kuma gwamnatin Shugaban Mahmood Abbas ta dora dukkan laifin abubuwan da suke faruwa a unguwar Shiekh Jarrah kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, wacce take son sauya yanayin birnin Qudus gaba daya.

342/